Bisa shirin kada kuri'un da gwamnatin kasar Sudan ta tsara, idan jama'ar yankin Darfur sun nuna goyon baya a hade jihohi 5, za a kafa kwamitin tsarin mulki mai 'yancin kai a wannan yankin, domin gudanar da harkokin hukumomin gwamnati a yankin Darfur. Idan kuma jama'ar sun ki amincewa, za a kiyaye jihohin biyar, sannan a wargaza hukumar wucin gadi wacce keda iko a wannan yanki. (Zainab)