Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da matakin dakarun kasar Afirka ta Tsakiya na tada hargitsi
Kwamitin sulhun MDD ya bayar da sanarwar shugaba a jiya Talata, wadda ke nuna damuwa game da tashe tashen hankula da ake zargin tawagar dakarun kasar Afirka ta Tsakiya da haifarwa, lamarin da ya tilastawa fararen hula masu yawa da gidajensu. Kaza lika sanarwar ta yi Allah wadai da hare-hare, da garkuwa da fararen hula da dakarun ke aikatawa.
Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin sulhun ya kalubalanci tawagar dakarun da su dakatar da ta da hargitsi, da cika alkawarin kawar da makamai, da kuma wanzar da zaman lafiya tsakanin al'umma. Kwamitin sulhun ya kuma jaddada goyon baya ga tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake kasar Afirka ta Tsakiya, bisa ayyukan da take gudanarwa, ciki hadda daukar matakan farko kan rundunar dakarun kasar. (Zainab)