An rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna dake da makasudin kula da manufofin dangantaka tsakanin kwamitin kolin 'yancin watsa labaru na kasar Congo da babban kwamitin sadarwa na rikon kwarya na jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, a ranar Jumma'ar da ta gabata a Brazzaville. Bangarorin biyu sun dauki niyyar girmama nauyin dake bisa wuyansu na hadin gwiwa wajen shirya kamfe cikin hadin gwiwa kan watsa labaru, ilimi da horo har ma da yin musanyar kwarewa ta fuskar bada tallafi ga shirye shiryen zabe da tsarin demukaradiya a cikin kasashen nasu biyu. (Maman Ada)