An samu muhimmin cigaba domin gudanar da bincike kan wadannan zarge zarge da tawagogin ma'aikatan MDD da dama da aka tura a wannan yanki suka gano a 'yan makwanni biyu da suka gabata, in ji mista Zeid, a cewar wata sanawa ta ranar Alhamis.
"MDD za ta yi iyakacin kokari domin gudanar da bincike kan wadannan zarge zarge na wuce gona da iri, da suka shafi wasu ayyukan fyade kan wani babban adadin mata da 'yan mata" in ji shi, tare da kara cewa "Muna daukar wadannan zarge zarge da muhimmanci, wasu daga cikinsu sun wuce gona da iri, kuma a maida hankali soasai.
A cewar sanarwar, yawancin zarge zargen sun shafi tawagar sojojin Burundi da Gabon dake yankin tsakanin shekarar 2013 da shekarar 2015, da kuma dakarun kasar Faransa na Sangaris da aka jibge lokacin kazamin tashin hankali a kasar. Haka zargin fyade a cikin sauran yankunan Afrika ta Tsakiya na cigaba da kasancewa abin da za a binciki a kai. (Maman Ada)