in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
HCR na nuna damuwa sosai da hare hare kan fararen hula a Afrika ta Tsakiya
2016-10-14 13:22:53 cri
Babbar hukumar 'yan gudun hijira ta MDD (HCR) ta bayyana matukar damuwarta game da hare hare kan fararen hula a jamhuriyar kasar Afrika ta Tsakiya (RCA) a ranar Alhamis, inda ake samun fito na fito tsakanin kungiyoyi masu gaba da juna, lamarin da kuma ya tilastawa miliyoyin mutane tserewa daga muhallinsu da janyo jinkiri ga ayyukan bada agaji. HCR ta yi allawadai da babbar murya da hare hare kan fararen hula da suka janyo cikas sosai ga isar da wani taimakon jin kai na gaggawa da al'ummomin dake cikin bukata, in ji wakilin HCR dake RCA, Kouassi Lazare Etien, a cikin wata sanarwa.

A cewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Afrika ta Tsakiya (MINUSCA), a kalla mutane 11 aka kashe kana wasu 22 suka jikkata a rikici tsakanin kungiyoyi daban daban masu dauke da makamai da suka biyo tare da kashe wani babban ofisa na rundunar sojin kasar a ranar 4 ga watan Oktoba, haka kuma har yanzu ba a da doriyar wasu mutane 14. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China