Kwmaitin sulhu na MDD ya tsawaita wa'adin sanya takunkumi ga wadanda suka lalata kwanciyar hankalin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Jiya Jumma'a ne, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da wani kuduri, inda ya tsawaita wa'adin takunkumi ga duk mutanen da suka lahanta kwanciyar hankali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da shekara guda, wato zuwa ranar 31 ga watan Janairun badi.
Kudurin ya bukaci kasashe daban-daban da su dauki duk wani matakin da ya wajaba, na kakabawa duk wadanda suka kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro a kasar Afirka ta Tsakiya takunkumin haramta sayar musu makamai da yin tafiye-tafiye, da kuma sanya musu haramcin yi amfani da kudadensu a banki.(Murtala Zhang)