A yayin tattaunawar, mutanen biyu sun amince da ra'ayin Sin da Afrika ta Tsakiya ya kamata su karfafa dangantakarsu kana kuma dangantaka tsakanin kasashen biyu tana da makoma mai haske.
Da yake godiya ga manzon musammun na kasar Sin game da zuwansa Afrika ta Tsakiya, shugaba Taoudera ya bayyana muhimmancin rawar da kasar Sin take takawa game da dangantakarta da Afirka ta tsakiya, inda ya kara da cewa dangantakar kasashen biyu ta kasance har kullum kan moriyar jama'ar kasashen biyu.
Da yake ambato sanarwar shugaba Xi Jinping a yayin dandalin Sin da Afrika na watan Disamban da ya gabata a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, mista Touadera na ganin cewa shugaba Xi ya baiwa Afrika wata tagar damammaki, da kuma Afrika ta Tsakiya take amfana.
Mista Zhang ya mika sakon taya murna na shugaba Xi ga mista Touadera kan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa. Ya ce, Kasar Sin a shirye take domin karfafa fahimtar juna da abokantaka tare da kasar Afirka ta tsakina kuma tana fatan dukkan bangarorin biyu zasu kara kokari domin karfafa dangantakar siyasa da sadarwa tsakanin al'ummomi.