in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika shinkafa ton 4, 000 ga Namibia
2017-04-05 10:34:37 cri
Kasar Sin ta mika Ton 4,000 na shinkafa a matsayin tallafi domin rage radadin fari ga kasar Namibia a birnin Windhoek.

An mika tallafin ne a hukumance tsakanin mataimakin ministan harkokin wajen Sin Zhang Ming da ya kai ziyara kasar, da mataimakiyar firayiministan Namibia kuma ministar harkokin wajen kasar, Netumbo Nandi-Ndaitwah.

Netumbo Nandi-Ndaitwah ta ce fari a Namibia ya shafi mutane sama da 595,000, inda shugaban kasar Hage Geingob ya ayyana shi a matsayin matsalar dake bukatar daukin gaggawa.

Ministar ta kara da cewa, wannan gagarumar gudunmawa ce, inda tuni aka aike da adadi mai yawa zuwa yankuna da wadanda aka bayar dominsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China