Taron mai taken: "auna kwayoyin cutar HIV da daukar sakamakon gwajin domin inganta tsarin", kasar Amurka ce zata dauki nauyin shirin, karkashin asusun fadar shugaban kasa na tallafin gaggawa game da yaki da cutar AIDS (PEPFAR).
Hukumar lafiya ta duniya ce ta amince da gwajin kwayoyin cutar kan wasu marasa lafiya dake dauke da kwayoyin cutar, wadanda ake musu magani ta hanyar canza musu jini.
Taron bitar shine irinsa na farko da aka taba gudanarwa a kasar Namibiya.Ana saran masana cutar ta HIV zasu tattauna da kuma yin musayar ra'ayoyi game da irin dabarun da kasashen su ke amfani dasu wajen dakile yaduwar cutar.
Kasar Namibiya guda ce daga cikin kasashen Afrika 3, da suka gudanar da mafi yawan gwajin kan marasa lafiya dake dauke da kwayoyin cutar ta HIV.
Gwajin kwayoyin cutar tare da daukar matakai nada matukar muhimmanci, kuma rashin daukar matakan na iya sa mutanen da suka kamu da cutar su galabaita, ko ya yi sanadiyyar mutuwarsu.(Ahmad Fagam)