in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibiya ta yi maraba da matakin kasar Sin na haramta safarar hauren giwa
2017-01-11 10:13:19 cri
Kungiyar kwararrun maharba ta kasar Namibiya (NAPHA), tare da sauran masana gandun daji, sun yi maraba da matakin da hukumomin kasar Sin suka dauka, na janye sarrafawa da kuma safarar hauren giwa sannu a hankali zuwa karshen shekarar 2017.

Babban kwamitin NAPHA, ya sanar a jiya Talata cewa, idan har wannan mataki aka aiwatar da shi, aka rufe kasuwannin hada hadar hauren giwa na kasar Sin, hakan zai tabbatar da ci gaba da wanzuwar giwaye a nahiyar Afrika kana ana fatan wannan haramci zai kuma shafi ragowar sassan jikin dabbobin.

A cewar kungiyar, wannan haramci na cinikin hauren giwar zai kasance mai matukar amfani ga gwamnatin kasar Namibiya da ma kungiyar maharban.

NAPHA ta ce adadin mafarautan kasar Sin ne mafiya karanci, idan aka kwatanta da na sauran kasashen duniya. Bugu da kari, adadin giwayen da ake farautarsu a duniya shi ne mafi karanci idan aka kwatanta da giwayen da suke mutuwa da karin kansu, da wadanda bil adama ke sanadiyyar hallaka su.

Kungiyar ta ce, wannan mataki, zai rage barazanar karewar giwaye a doron kasa.

Haka zalika, NAPHA ta lura cewa, duk wannan yunkuri da kasar Sin ta yi, kasuwar hada hadar hauren giwa ta kasar Sin ita ce ke sahun baya idan aka kwatanta da irin barazanar da giwaye ke fuskanta a Afrika, wanda ya hada da hasarar muhalli, matsalolin da bil adama ke haifarwa da farautar namun daji, kuma dukkan wadannan ba zai shafi haramcin da kasar Sin din ta yi ba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China