in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Amurka da na Masar sun alkawarta hadin gwiwa wajen yakar ta'addanci
2017-04-04 12:51:00 cri

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaran sa na Masar Abdel Fattah El-Sisi, sun sha alwashin marawa juna baya, wajen yaki da dukkanin wani nau'i na ayyukan ta'addanci. Shugabannin biyu sun yi wa juna wannan alkawari ne a jiya Litinin, yayin wata ganawa da suka yi a birnin Washington.

Da yake tsokaci yayin ganawar tasu, shugaba Trump ya ce duk da yake kasashen biyu na da sabani a 'yan wasu batutuwa, amma ya gamsu da yadda shugaba El-Sisi ya amince da marawa Amurka baya kan muhimman batutuwa masu yawa.

Shi ma a nasa bangare El-Sisi, cewa ya yi ya gamsu da aniyar Amurka, ta daukar matakan duk da suka wajaba, a fannin yaki da ta'addanci daga dukkanin fannoni. Ya kuma alkawarta kudurin kasar sa na marawa Amurka baya a wannan fanni. Ya ce yana da imanin gwamnatin Amurka mai ci, za ta kai ga cimma nasarar da take fata a fannin yaki da ta'addanci.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China