Fadar White House ta ce shugaban Amurka Donald Trump na sa ran ganawa da takwaransa na kasar Sin Xi Jingping, da za ta inganta hulda a tsakaninsu.
Sanarwar da kasashen biyu suka bada a jiya Alhamis, ta ce Shugabannin biyu za su yi ganawarsu ta farko ne tun bayan da Trump ya kama aiki a watan Janairu, a fadar Mar-a-Logo na jihar Florida, a ranakun 6 da 7 na watan Afrilu.
Yayin wani taron manema labarai, kakakin fadar White House Sean Spicer ya ce, yayin ganawar ta Shugaba Trump da Shugaba Xi, za su yi masayar ra'ayoyi kan al'amuran da suka fi bawa muhimmanci da kuma inganta huldar dake tsakanin kasashensu.
Har ila yau, ya ce za kuma su tattauna, kan batutuwan da suka shafe su, ciki har da batun Koriya ta Arewa da cinikayya da kuma tsaron yankunansu. (Fa'iza Mustapha)