in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da sabon matakin takunkumin da za ta yi wa Korea ta Arewa
2017-04-01 13:31:08 cri

Ma'aikatar kula da baitulmalin Amurka ta sanar da cewa, za ta kakabawa wani kamfanin cinikayya da wasu mutane 11 'yan asalin kasar Korea ta Arewa takunkumin tattalin arziki, bisa dalilin cewa, kamfanin da wadannan mutane su na goyon bayan aikin nazari domin kera makaman nukiliya da makamai masu linzami a kasar ta Korea ta Arewa.

Sanarwar da ma'aikatar ta bayar Jiya Jumma'a, ta ce, mutanen 11, su ne jami'an ofisoshin dake wakilci a kasashen waje, na bankuna da kamfanonin cinikayya da kamfanonin jiragen ruwa masu jigilar kayayyaki na Korea ta Arewa.

Sanarwar ta bayyana cewa, mutanen da za a kakabawa takunkumin, su na aiki ne a kasashen waje a madadin gwamnatin Korea ta Arewa, sannan, su na hidima tare da samar da kudi ga kamfanonin kera makaman kare dangi na kasar, da MDD da Amurka suka sanyawa takunkumi.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China