in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana neman wanda ya kai farmaki wani gidan rawa a Amurka
2017-03-27 11:11:28 cri
Wani mataimakin shugaban 'yan sanda a Amurka, Paul Neudigate ya ce har yanzu ba a kai ga gano mutmin da ya kai famaki wani gidan rawa a birnin Cincinnati na jihar Ohio ba, harin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum guda tare da raunata wasu 14.

Paul Neudigate ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa zuwa yanzu dai, mutum guda ake zargi da kai harin, inda a ke ci gaba da binciken ko akwai wasu dake da hannu ciki.

Da farko, 'yan sanda a Cincinnati sun ce akalla mahara biyu ne suka bude wuta a gidan rawar Cameo da misalin karfe 1 na daren Lahadi agogon GMT.

Jami'in Dan sandan a jiya da safe ya sake wallafawa a shafinsa na tweeter cewa, babu wata alama dake nuna cewa harin na ta'addanci ne, ya na mai cewa har yanzu ba a san manufarsa ba.

Ya kuma shaidawa gidan talabijin na WLWT cewa daruruwan mutane ne a cikin gidan rawar lokacin da al'amarin ya auku.

'Yan sandan dai sun ce, akwai camarorin sa'ido a cikin gidan rawar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China