A yau Laraba ne aka kaddamar da shirin horar da manema labaru karo na 4, a cibiyar musayar ra'ayi tsakanin Sin da Afirka ta fuskar watsa labaru dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Shugaban majalissar harkokin diplomasiyyar al'umma ta kasar Sin mista Li Zhaoxing, ya halarci bikin kaddamar da taron, inda ya kuma gabatar da jawabi.
Cikin jawabin na sa, Mr. Li yayi fatan cewa, manema labaru na kasashen Afirka wadanda suka halarci shirin, za su kara fahimtar manufar kasar Sin, da samar da gudunmawa ga hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar watsa labaru.
Kaza lika a wajen taron, ma'aikaciyar jaridar "The Leadership" ta tarayyar Najeriya Bukola Ogunsina, ta gabatar da jawabi a madadin sauran manema labaru na kasashen Afirka, inda ta ce za su yi amfani da wannan dama, domin nazari kan ilimin da ya shafi kasar Sin, da harkar watsa labaru, ta yadda za su kasance masu taimakawa musayar ra'ayi tsakanin Sin da nahiyar Afirka. (Bello Wang)