in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya fitar da alkaluman kudin musayar RMB da aka adana a fadiin duniya
2017-04-01 12:12:12 cri

A karon farko, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar da alkaluma game da yanayin da ake ciki a fannin adana kudin musanya na RMB a fadin duniya.

Alkaluman da IMF ya fitar Jiya Jumma'a, ya nuna cewa, ya zuwa rubu'i na hudu na bara, adadin kudin musanyar RMB da aka adana ya kai dalar Amurka biliyan 84 da miliyan 510, adadin da ya kai kaso 1.07 bisa dari idan aka kwatanta da adadin kudin musayar daukacin kudaden da aka yi kididdigar su.

Alkaluman sun nuna cewa, ya zuwa rubu'i na hudu na bara, kwatankwacin adadin kudin musanyar da aka adana a fadin duniya ya kai dalar Amurka biliyan dubu 10 da dari 7 da casa'in, adadin da bai kai na rubu'i na uku na bar aba, wanda ya kai dalar Amurka biliyan 11 da sittin.

Tun daga watan Oktoban bara ne asusun IMF ya fara gudanar da bincike kan yanayin da ake ciki a fannin adana kudin musanya na RMB a fadin duniya.

Kafin wannan, IMF ya taba bayyana cewa, matakin da aka dauka zai kara kyautata alkaluman da za a samu game da adana kudin musanya na RMB a fadin duniya, karkashin kokarin da kasar Sin ke yi wajen yi wa harkokin cinikayya kwaskwrima, kana zai karfafawa gwamnatocin kasashen duniya gwiwar kara adana kudin RMB a kasashensu.

A halin da ake ciki yanzu, kasashe da yankuna 146 a fadin duniya sun gabatar da alkalumansu ga IMF, inda kasar Sin ita ma ta fara samar da alkalumanta ga IMF tun daga watan Satumban shekarar 2015, wanda mataki ne da gwamnatin kasar ta dauka na kyautata tsarin kudinta.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China