A cikin sanarwar, babban bankin kasar Sin ya bayyana cewa, a 'yan kwanaki, kasuwannin cinikin kudaden duniya sun samu sauye-sauye sosai sakamakon ballewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar Turai EU. Lamarin ya kuma sa darajar kudin RMB ta samu dan raguwa. Amma yanzu ana cinikin kudin RMB a kasuwa bisa dokokin da aka tsara kamar yadda ya kamata. Darajar kudin RMB ba ta samu sauye-sauye sosai ba.
Sannan, wannan sanarwa ta ce, an yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun bunkasa cikin sauri, kuma yana da karfin yin takara a duniya gaba daya. Bugu da kari, kasar Sin tana da isassun kudaden waje da ta ajiya da kasafin kudi. Kasar Sin ba ta da shirin rage darajar kudin RMB domin kara karfin takara domin fitar da kayayyakinta zuwa kasashen duniya. Halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki ya alamanta cewa, babu wani dalilin rage darajar kudin RMB da zai kasance cikin dogon lokaci a nan gaba ba. (Sanusi Chen)