in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shigar da kudin RMB a cikin tsarin SDR a hukunce
2016-10-01 13:26:38 cri
A jiya ranar 30 ga watan Satumba, shugabar asusun bada lamuni na duniya wato IMF Christine Lagarde ta sanar da cewa, tun daga ranar 1 ga watan Oktoba, an sabunta tsarin SDR a hukunce.

Christine Lagarde ta yi nuni da cewa, wannan ne babban canji bayan da kudin Euro ya shiga tsarin SDR, wannan yana da babbar ma'ana ga tsarin SDR, asusun IMF, kasar Sin da kuma tsarin hada-hadar kudi na duniya.

Shigar da kudin RMB ya sabunta tsarin SDR na asusun IMF, wanda ya sa tsarin SDR ya kara wakilaci kudaden duniya da tattalin arzikin duniya, kana ya shaida ci gaban da aka samu kan kwaskwarima da aka yi wa tsarin kudin Sin, da musayar kudade da hada-hadar kudi, kana kasa da kasa sun nuna amincewa ga wannan ci gaba.

Asusun IMF ya kafa tsarin SDR a shekarar 1969 don taimakawa kasashe membobin kungiyar da su adana kudi. Shigar da kudin RMB a cikin tsarin SDR ya shaida canjan tsarin tattalin arzikin duniya, shaida samun ikon fada a ji a tsakanin wasu kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki a tsarin hada-hadar kudi na duniya, kana ya mayar da martani ga kasa da kasa da suka bukaci da yin kwaskwarima kan tsarin hada-hadar kudi na duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China