Mrs Lagarde a cikin sanarwa ta ce kwararrun ma'aikata, a cikin rahoton su ga hukumar zartaswar asusun sun tabbatar da cewa kudin RMB na kasar Sin a yanzu ya cimma ka'idojin yin amfani da shi a ko ina.
Kudin da ake kira Yuan ko Renmimbi ya gaza cimma tsarin SDR a shekara ta 2010 a sakamakon da asusun ta fitar wannan lokacin wanda ya zama wajibi a matsayin da ake bukata in har ana son a shigar da shi wannan kwandon na SDR.
A matsayin kudaden dake jagoranta ciniki a kasuwannin duniya, kwandon na SDR a yanzu haka yana da kudin Dalar Amurka, Euro na Turai, Yen na Japan, da kuma Fan na Ingila. (Fatimah Jibril)