in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin jama'ar Sin ya yi maraba da kudurin IMF na shigar da kudin RMB cikin tsarin SDR
2015-12-01 10:42:33 cri
Bankin jama'ar kasar Sin ya sanar a yau Talata cewar, ya yi maraba da kwamitin gudanarwar hukumar bada lamani ta IMF sakamakon amincewa da kudurin shigar da kudin RMB na kasar Sin cikin tsarin ikon Special Drawing Rights wato SDR a takaice.

A ranar 30 ga watan Nuwanba ne, kwamitin gudanarwar hukumar ta IMF ya tsaida kudurin shigar da kudin na RMB cikin tsarin SDR, don haka a halin yanzu, tsarin na SDR ya kunshi kudade nau'i 5 da suka hada da Dalar Amurka da kudin Euro, da RMB na kasar Sin, da kudin Japan, da kuma Ponds na Ingila.

Sanarwar ta bayyana cewa, wannan mataki ya nuna cewar, an gamsu da irin rawar da kasar Sin ke takawa wajen raya tattalin arziki da yin kwaskwarima da bude kofar hulda da kasashen duniya. Kuma kasar Sin ta yabawa shugabannin hukumar ta IMF da ma'aikatanta wadan da suka yi kokarin gudanar da aikin yin bincike, da kuma kasashe membobin hukumar da suka nuna goyon baya ga kasar Sin. Shigar da kudin RMB a cikin tsarin ikon SDR zai sa kaimi ga kara wakilcin SDR, da kyautata tsarin kudi na duniya a halin da ake ciki a yanzu, wanda ya samar da moriya ga kasar Sin har ma ga dukkan duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China