A 'yan kwanan baya ne ministan harkokin wajen kasar Chadi Moussa Faki Mahamat ya kama aiki a matsayin sabon shugaban kwamitin zartaswa na kungiyar hadin kan Afirka ta AU.
Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya shaida wa taron manema labaru yau Jumma'a a Beijing cewa, kasar Sin na fatan inganta hadin gwiwa da Moussa Faki Mahamat da sabon kwamitin AU, a kokarin kara azama kan huldar da ke tsakanin Sin da AU, da ma tsakanin Sin da nahiyar Afirka. (Tasallah Yuan)