Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang, shi ne ya tabbatar da hakan a yayin taron manema labarai da aka gudanar a yau Alhamis. Da yake amsa tambayar da aka gabatar masa, game da hulda Sin da Amurka a fannin cinikayya, Mr. Lu ya ce alakar kasashen biyu a wannan fanni na ba da damar cin moriyar juna.
Ya ce Sin na fatan kara hada kai da Amurka wajen fadada harkokin cinikayya, tare da magance sabanin dake tsakanin ta hanyar shawarwari. Kaza lika Sin na da burin ganin sassan biyu sun ci gaba da raya mu'amala cikin kyakkyawan yanayi, wanda hakan ka iya haifar da ci gaban cinikayya, da bunkasar tattalin arzikin su tare.
Wannan ne dai karon farko da shugaba Xi zai zanta da Mr. Trump kai tsaye, tun bayan kama aikin shugaba Trump a matsayin shugaban Amurka a watan Janairun da ya gabata. (Saminu Hassan)