A yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing.
Xi Jinping ya jaddada cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana da muhimmanci sosai ga kasashen biyu har ma ga dukkan duniya baki daya. Ya ce kamata ya yi bangarorin biyu su kara yin imani da juna da fahimtar juna. Moriyar kasashen biyu ta fi matsalolinsu, hadin gwiwa hanya daya da ta fi dacewa ga bangarorin biyu. Ya kamata a duba dangantakar dake tsakaninsu daga manyan tsare-tsare, da fadada hadin gwiwarsu don samun moriyar juna. Kana za a kara yin mu'amala da juna kan manyan batutuwan shiyya-shiyya, da girmama moriyarsu, da tabbatar da kiyaye dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.
A nasa bangare, Tillerson, ya bayyana cewa, shugaba Trump yana begen yin ganawa a tsakaninsa da shugaban kasar Sin, da kai ziyara a kasar Sin, don tabbatar da makomar bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a shekaru 50 masu zuwa. Kasar Amurka tana son raya dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu bisa ka'idojin daina nuna kiyayya ga juna, da nuna fahimtar juna, da girmama juna, da yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, don tinkarar kalubalolin da kasa da kasa ke fuskanta. (Zainab)