A cikin sakon, Xi ya nuna cewa, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin Sin da Jamus na bunkasa cikin sauri, kuma manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu na kara mu'amala da cudanya tsakaninsu, kana hadin-gwiwarsu na zurfafa a fannoni daban-daban. Xi ya jaddada cewa, inganta hadin-gwiwa tsakanin Sin da Jamus, ba ma kawai zai samar da alfanu ga al'ummomin kasashen biyu ba ne, har ma zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya, da tabbatar da kwanciyar hankali, gami da samun wadata a fadin duniya.
Xi ya ce, yana fatan nuna himma da kwazo tare da Frank-Walter Steinmeier, a kokarinsa na kara raya huldar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare daga dukkanin fannoni.(Murtala Zhang)