in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai kai ziyara kasashen Finland da Amurka
2017-03-30 15:50:45 cri
A makon gobe ne Shugaban kasar Sin Xi Jingpin, zai kai ziyarar aiki kasar Finland, sannan ya wuce jihar Florida ta kasar Amurka, domin halartar tattaunawar da za su yi da shugaba Donald Trump na kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang ne ya sanar da haka, lokacin da yake ganawa da manema labarai a yau Alhamis.

Lu Kang ya ce bisa gayyatar da Shugaba Sauli Niinisto na Jamhuriyar Finland da Shugaba Donald Trump na Amurka suka yi masa, Shugaba Xi, zai kai ziyara Finland daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Afrilu, sannan ya zarce zuwa Amurka, inda zai gana da Shugaba Trump a fadar Mar-a-Logo dake Florida a ranakun 6 da 7 ga watan na Afrilu. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China