in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Madagascar
2017-03-27 21:19:04 cri

A yau Litinin a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Madagascar Hery Rajaonarimanmpianina.

A yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya bayyana cewa, bangaren Sin na tsaiwa tsayin daka kan manufar bunkasa huldar abokantaka irin ta sada zumunci daga dukkan fannoni da kasashen Afirka, kuma zai ci gaba da bin ka'idojin nuna sahihanci da zihiri da zumunci, da aminci, da daidai tunanin nuna adalci, da samun moriya a lokacin da yake mu'amala da kasashen Afirka. Bugu da kari, zai aiwatar da manufofin da aka tsara a yayin taron kolin dandanlin hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka da aka yi a Johnnesburg na kasar Afirka ta kudu. Sannan a lokacin da yake neman ci gaba, tabbas bangaren Sin zai kula da matakan neman dauwamammen ci gaban kasashen Afirka, ta yadda kasar Sin da kasashen Afirka za su iya samun nasara tare, da kuma samun ci gaba tare.

A nasa bangaren, Mr. Hery ya bayyana cewa, bangaren Madagascar ya yaba da jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi, a yayin taron tattaunawar tattalin arziki na Davos da aka shirya a watan Janairun bana, yana kuma nuna goyon bayan shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kasar Sin. Bugu da kari, yana fatan za a kara yin hadin gwiwa tsakanin kasarsa da kasar Sin a fannonin samar da makamashi, da zirga-zirgar jiragen sama, da jigilar kayayyaki, da ayyukan gina madatsun ruwa, da filayen saukar jiragen sama. Ya ce Madagascar za ta kuma kara yin mu'amala da bangaren Sin kan harkokin kasa da kasa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China