Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana alakar dake tsakanin Sin da Australia, a matsayin budaddiyar alaka da ba ta da wata boyayyiyar manufa, kuma ba a kafa ta domin ta haifar da adawa da wata kasa ba.
Mr. Li wanda ya bayyana hakan a Juma'ar nan, a ci gaba da ziyarar aiki da yake yi a kasar Australia, ya ce tun tuni kasar Sin ke maimaita kudurin ta, na daukar kasashen duniya bai daya a fannin hadin gwiwar samar da ci gaba, ba tare da la'akari da girma ko kankantar su ba.
Firaministan na Sin wanda ke magana yayin wani taron manema labarai tare da takwaransa na Australia Malcolm Turnbull, bayan ganawar shekara shekara da suka yi a birnin Canberra, ya kara da cewa Sin na martaba da dukkanin kasashen duniya, za kuma ta ci gaba da raya dangantaka da kowa bisa daidaito.
Daga nan sai ya yi fatan cewa, baya ga alfanun dangantakar Sin da Australia, a hannu guda alakar kasashen 2 ba za ta cutar da sauran kasashen duniya ba.(Saminu Alhassan)