in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya halarci liyafar da takwaransa na Australia ya kira
2017-03-24 12:56:51 cri

A ranar 23 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci liyafar da takwaransa na kasar Australia Malcolm Turnbull ya shirya masa a babban ginin majalisar dokoki dake birnin Canberra na kasar, haka kuma, 'yan majalisun dokokin kasar, da wakilai na kamfanoni, da na bangarorin kimiyya da fasaha da ilmi da kuma jakadun kasashen ketare dake kasar Australia kimanin dari hudu ne suka halarci liyafar.

Li Keqiang ya ba da jawabi a yayin wannan liyafa, inda ya bayyana cewa, Sin da Australia suna hulda da hadin gwiwa sosai da juna, kuma ya kai wannan ziyarar aiki kasar domin inganta harkokin ciniki cikin 'yanci, ta yadda za a karfafa bunkasuwar tattalin arziki da kuma warware matsalolin da za a gamu da su bisa ci gaban da aka samu.

Ya kara da cewa, wani dalili daban na wannan ziyararsa zuwa kasar Australia kuma shi ne domin inganta zaman lafiya da zaman karko na yankin, sabo da ya zama dole a tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a shiyya shiyya da ma duniya baki daya idan ana son raya tattalin arziki da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummar kasa da kasa.

Haka zalika, ya ce, ya zo ziyarar aiki a kasar Australia ne domin karfafa mutunta juna, hadin gwiwa da kuma mu'amalar al'adu a tsakanin kasashen biyu, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen bin manufar diflomasiyya ta kiyaye 'yanci kai da zaman lafiya, yayin da neman bunkasuwar kasar bisa hanyoyin da suka dace da halin kasar. Dangane da yadda za a warware matsalolin da za a gamu da su, Li Keqiang ya ce, ya kamata a warware matsalolin bisa ka'idojin siyasa da na tattalin arziki na da kuma ra'ayi daya da aka cimma a tsakanin kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China