Firaiministan kasar Sin Li Keqiang ya bukaci a samar da wadatattun kayayyakin aikin gona da nufin ingantawa da kuma habaka ci gaba fannin na aikin gona.
Cikin wani umarni da ya bayar a lokacin taron jama'a game da sha'anin aikin gona a jiya Laraba, Li, ya bukaci shugabannin kananan hukumomi da su kara kaimi wajen bunkasa ci gaban aikin gona, kana ya jaddada muhimmancin bunkasa ci gaban yankunan karkara da kara samar musu da kudaden shiga.
Firaiministan na Sin ya ce, lokacin bazara yanayi ne da ya dace da aikin gona, don haka ya ce akwai bukatar kananan hukumomi su samar da kayayyakin aiki, da ingantattun irin shuka, kuma su zauna cikin shirin ko ta kwana game da tunkarar duk wani sauyin yanayi na fari ko ambaliyar ruwa, kana su jajurce wajen inganta fannin hasashen yanayi.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta nace kan manufarta ta samar da ingantattun kayayyakin amfanin gona wadanda za su iya yin gogayya a kasuwanni.(Ahmad Fagam)