in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu tagomashi a fannin kirkire-kirkiren kimiyya a 2016
2017-01-09 09:40:06 cri

Kasar Sin ta samu matukar bunkasuwa a shekarar da ta gabata, kama daga kimiyyar yanar gizo zuwa batun binciken sararin samaniya karkashin shirin kirkire-kirkiren kimiyya na kasar Sin nan da shekara ta 2020.

Sakamakon samar da tsarin sadarwa na shiga yanar gizo, wanda masana kimiyyar kasar Sin suka yi, hakan ya kawo gagarumin ci gaba wajen baiwa mutane masu yawa samun damar shiga yanar gizo a shekarar 2016. Ya zuwa karshen watan Nuwambar bara, kasar Sin ta samar da tsarin sadarwa mai sauri na 4G ga masu amfani da wayar salula kimanin miliyan730, kana an samu masu amfani da tsarin sadarwa na shiga yanar gizo kusan mutane miliyan 300.

Wannan ci gaba da aka samu ya faru ne sakamakon tallafin da gwamnatin kasar Sin ta ba da.

Kasar Sin ta kebe kimanin yuan biliyan 24.8 kwatan kwaci dalar Amurka biliyan 3.6 a fannin bunkasa kimiyyar kasar a kasafin kudinta na shekarar 2016, adadin da ya zarta na shekarar 2015 da kashi 11.9 bisa dari.

A yayin da kasar Sin ta koma kan tsarin fasahar kirkire kirkire, a shirye take ta sake samun matukar bunkasuwa a nan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China