An dai harba wadannan taurarin dan adam ne daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan, wadda ke arewa maso yammacin kasar Sin. Kaza lika masu kula da aikin sun ce rokar Kuaizhou-A1 sabon samfuri ce ta Kuaizhou-1 wanda aka yi wa kwaskwarima, tare da kara wasu fasahohi na inganta aikinta, tana kuma iya harba tauraron dan adama da bai kai nauyin kilogiram 300 ba zuwa samaniya.
Daya daga kumbunan da aka harba wato JL-1 na aikin nazarin sassan duniya ne, yana kuma iya daukar hotunan bidiyo da ake amfani da su, wajen safiyon albarkatun kasa da gandayen daji, da aikin kare muhalli, da kuma harkar sufuri. Sauran fannonin sun kunshi ayyukan kare aukuwar bala'u da kuma na ba da agaji. (Saminu Hassan)