A yayin taron manema labarai da aka shirya, Mr. Spicer ya bayyana cewa, an fitar da wannan umurni ne da zummar kawar da cikas ta fuskar amfani da makamashi a kasa, ta yadda za'a inganta tsaron makamashi a Amurka.
Spicer ya jaddada cewa, sabon umurnin zai baiwa Amurkawa damar amfani da makamashi, gami da wutar lantarki mai tsabta kuma cikin farashi mai rahusa.
A karshe, zai taimaka ga habakar tattalin arziki, da samar da guraban ayyukan yi a fadin kasar.
Tuni, sabon shugaban hukumar kare muhalli ta Amurka, Scott Pruitt, ya nuna cewa, umurnin zai kawar da shirin raya makamashin wutar lantarki mai tsabta da gwamnatin Obama ta bullo da shi a shekara ta 2015, wanda ya kasance shiri mafi muhimmanci, a manufar sauyin yanayi ta gwamnatin Obama.
Shi dai Mr. Trump ya taba bayyana sauyin yanayi a matsayin karya, kuma a yayin da yake yakin neman zaben sa, ya yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar Paris ta MDD kan batun tinkarar sauyin yanayi. (Murtala Zhang)