in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya rattaba hannu kan takardar dake bada umarnin Amurka ta janye daga yarjejeniyar TPP
2017-01-24 10:46:30 cri
Shugaban Amurka Donald Trump, a jiya Litinin, ya rattaba hannu kan wata takardar dake bada umaranin Amurka ta janye daga yarjejeniyar cinikayya dake tsakanin kasashen yankin Fasifik.

Trump ya bayyana matakin a masayin wani muhimmin abu ga ma'aikatan Amurka, inda ya ce an dade ana magana kan batun.

Yarjejeniyar TPP, yarjejeniyar cinikayya ce cikin 'yanci da aka kulla tsakanin kasashe goma sha biyu na yankin Asia da Fasifik, wadda ministocin daga kasashen suka sanyawa hannu a watan Fabrerun bara, bayan shafe sama da shekaru biyar ana kulla yarjejeniya.

Wannan umarni na shugaba Trump ba zai yi aiki nan take ba, domin majalisar dokokin kasar ba ta amince da bukatar ba tukuna.

Sai dai, wnnnan alama ce dake nuna cewa sabuwar gwamnatin na sauya ka'idojin cinikayyar kasar.

Manufofin cinikayya da gwamnatin Trump ta sanya a gaba sun fara ne daga janyewa daga yarjejeniyar TPP da kuma sake kulla yarjejeniyar cinikayya da kasashen nahiyar Arewacin Amurka.

A lokacin da yake yakin neman zabe, Donald Trupmp ya yi alkawarin ba zai taba kulla yarjejeniya makamanciyar TPP ba, wanda ya bayyana a matsayin abun da ka iya durkusar da masana'antun Amurka, inda ya lashi takobin sake kulla yarjejeniyar cinikayya da kashen nahiyar arewacin Amurka, yana mai barazanar sanyawa Mexico haraji mai tsauri. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China