Sanarwar ta kara da cewa, wannan umarni tamkar nuna wariya ne saboda bambancin kasa da ya nuna, kuma hakan zai haddasa kara nuna kyama ga mabiya addinin musulunci. Sanarwar dai wanda wakilai na musamman na MDD suka ratattabawa hannu, da suka hada da wakilin musamman na sahen kula da bakin haure, Francois Crepeau; da na sashen nuna wariya Mutuma Ruteere; da na kare hakkin dan adam da yaki da ta'addanci, Ben Emmerson; da sashen muzgunawa, Nils Melzer; da kuma na sashen 'yancin addini, Ahmed Shaheed.
A yayin da shugaban Amurka ya bada umarnin dakatar da shirin 'yan gudun hijira na kwanaki 120, masanan sun bayyana cewa a daidai wannan lokacin da duniya ke fuskantar karuwar 'yan gudun hijira mafi yawa da ba'a taba fuskantar irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu, wannan babban koma baya ne musamman ga mutanen dake neman kariya ta kasa da kasa.
Kwararrun sunce wajibine Amurkar ta samar da kariya ga mutanen da rikici ya daidaita.