in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun Amurka ta yi watsi da bukatun gwamnatin Trump na janye hukuncin Robart
2017-02-06 10:54:51 cri
A sanyin safiyar jiya Lahadi ne kotun daukaka kara ta tara, ta tarayyar Amurka ta fitar da sanarwa, inda ta yi watsi da bukatun ma'aikatar shari'a ta kasar, game da hukuncin James Robart, matakin da ke nuni cewa, ba za a aiwatar da haramcin da sabon shugaban kasar Donald Trump ya yi umarni ba, game da dakatar da shigar 'yan gudun hijira, da ma 'yan wasu kasashen musulmi bakwai cikin Amurka.

A ranar 3 ga wata, mai shari'a James Robart na kotun gundumar yammacin Washington, ya yanke hukuncin daina aiwatar da haramcin da gwamnatin Trump ta sanya, hukuncin da ya fara aiki nan take. Kashegari kuma, sashen shari'a na kasar ya sanar da daukaka kara. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China