
A jiya da dare ne shugaban Amurka Donald Trump ya kori mai rikon mukamin antoni janar ta kasar Sally Yates daga mukaminta, sa'o'i bayan da ta umarci sashen shari'a na kasar da kada ya goyi bayan shirin Trump din game da hana 'yan gudun hijira da musulmi daga wasu kasashe shiga kasar, matakin da ya haifar da zanga-zanga da suka daga sassa daban-daban na duniya.(Ibrahim)