in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon antoni-janar din Amurka na rikon-kwarya zai aiwatar da haramcin shigar baki kasar
2017-01-31 16:45:47 cri
Bayan da ya kama aiki a daren jiya Litinin, ba tare da wani jinkiri ba, sabon antoni-janar din kasar Amurka na rikon-kwarya Dana Bent, ya fitar da wata sanarwa, inda ya sanar da soke umarnin da tsohuwar antoni-janar ta rikon-kwarya Sally Yates ta bayar, na kin amincewa da haramcin shigar wani rukuni na baki cikin Amurka. Mr. Dana Bent ya kuma bukaci lauyoyi da su kare umurnin da shugaba Trump ya bayar.

A baya dai Sally Yates ta bayyana cewa, hukumarta ba za ta bada kariya ga haramcin shigar bakin Amurka ba, saboda a ganinta, matakin da Trump ya dauka ya sabawa doka. Sai dai daga bisani, Trump ya kore ta daga mukamin na ta, ya kuma maye gurbin ta da Dana Bent, a matsayin sabon antoni-janar din Amurka na rikon-kwarya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China