in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi makokin mutanen da suka mutu a sakamakon fashewar bom a kasar Turkiya
2016-12-12 11:00:28 cri

Firaministan kasar Turkiya Binali Yildirim ya gabatar da sanarwa a jiya Lahadi wadda ke bayyana wannan rana a matsayin ranar juyayi a dukkanin fadin kasar, game da mutanen da suka mutu a sakamakon fashewar bom a birnin Istanbul na kasar a ranar 10 ga wannan wata.

A jiyan ne kuma aka yi makokin wadanda suka rasu a birnin Ankara da Istanbul, kana dukkan hukumomin gwamnatin kasar, da ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen waje sun sassauto da tutar su kasa don nuna alhini.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiya Suleyman Soylu ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, ya zuwa yanzu, mutane 38 ne aka tabbatar da rasuwar su sakamakon fashewar bom din na ranar 10 ga wata, ciki har da 'yan sanda 30, kana mutane 155 su samu raunuka, ciki hadda 14 da raunukan su suka tsananta.

Kungiyar TAK ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren fashewar boma-bomai biyu a daren ranar ta 10 ga wata a birnin Istanbul. A daya hannun kuma mutane fiye da dubu daya sun yi zanga-zangar Allah wadai da wannan aiki na ta'addanci a birnin Istanbul.

A wani ci gaban kuma, a jiya Lahadi, shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin ya buga waya ga shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan, inda shugaban Putin ya bayyana jajen sa ga rasuwar 'yan kasar ta Turkiyya sakamakon aukuwar harin, yana mai cewa harin na ta'addanci a birnin Istanbul laifi ne da masu aikata shi ba su yi la'akari da mummunan sakamakon sa ba.

Har wa yau a dai wannan rana, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana a gun taron majalisar ministocin kasar sa cewa, Isra'ila na Allah wadai, da duk wane nau'i na aikin ta'addanci a kasar Turkiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China