in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun PKK sun sanar da daukar alhakin kai hari ga ofishin 'yan sandan kasar Turkiya
2016-08-20 13:16:25 cri
Dakarun PKK sun sanar ta hanyar shafinsu na internet a jiya ranar 19 ga wata cewa, kungiyarsu ta kai harin bom kan 'yan sanda a gabashin kasar Turkiya a ranar 18 ga wata.

An kai harin bom da aka dasa cikin mota kan cibiyar ofishin 'yan sandan birnin Elazig dake jihar Elazig ta gabashin kasar Turkiya, wanda ya haddasa mutuwar 'yan sanda 3, yayin da mutane 217 ciki har da 'yan sanda 85 suka ji rauni. Ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiya ya bayyanawa 'yan jarida a ranar 19 ga wata cewa, bisa binciken da 'yan sanda suka yi, ya nuna cewa wani dan kasar Turkiya, ya kai harin ta hanyar dasa bom a cikin wata motar bas.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Turkiya suka bayar, an ce, mutane fiye da dubu daya na birnin Elazig sun yi zanga zanga don nuna adawa ga dakarun PKK da suka kai harin ta'addanci.

Tun daga daren ranar 17 zuwa 18 ga wata, an kai hare-haren boma-bomai ga 'yan sanda ko sojoji a jihohin Van, Elazig, Bitlis dake gabashin kasar Turkiya, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 12 tare da raunatar mutane kimanin 300. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China