An yi bikin mika takardar kama aikin sabon jakadan a fadar shugaban kasar Isra'ila.
Da yake jawabi yayin bikin, Mr. Okem ya bayyana cewa, hakan sabon mafari ne na raya dangantakar dake tsakanin Turkiya da Isra'ila.
Shi kuwa a nasa bangare, shugaba Rivlin cewa ya yi, wannan muhimmin lokaci ne a tarihi, yana kuma fatan kasashen biyu za su ci gaba da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya da dai sauransu. Kaza lika Mr. Rivlin ya jajantawa jama'ar Turkiya bisa harin ta'addanci da ya auku a birnin Istanbul a ranar 10 ga wata.
Kafin hakan, jakadan kasar Isra'ila dake kasar Turkiya ya riga ya isa kasar Turkiya, tuni kuma ya fara gudanar da aikinsa. (Zainab)