in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai harin roka kan filin jirgin sama na birnin Diyabakir dake kudu maso gabashin Turkiya
2016-08-28 14:06:48 cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Anadolu na Turkiya ya bayar, an ce, a daren jiya Asabar, an kai harin rokoki har 4 kan wata tashar bincike ta 'yan sanda a filin jirgin sama na birnin Diyabakir da ke kudu maso gabashin kasar. Wani jami'i ya bayyana cewa, kawo yanzu babu rahoto dangane da adadin mutanen da suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata.

An ba da labarin cewa, hukumar kula da filin jirgin saman kasar ta kwashe fasinjoji da ma'aikata zuwa wani yanki daga filin jirgin saman cikin gaggawa.

Sai dai ana nuna tababa game da ko dakaru masu dauke da makamai na jam'iyyar Kurdistan ne suka kai wannan hari. 'Yan sandan kasar na cigaba da kokarin zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China