in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar Chadi ta kaddamar da shirin yaki da cutar polio
2017-03-26 12:33:03 cri
Ma'aikatar lafiya ta jamhuriyar Chadi a jiya Asabar, ta kaddamar da shirin allurar riga-kafin cutar polio a duk fadin kasar.

Shirin riga-kafin wanda za a shafe kwanaki 4 ana gudanar da shi, ana sa ran yiwa yara miliyan 3 da dubu 300 'yan kasa da shekaru 5 alluran riga-kafin a duk fadain kasar.

Kasar Chadi ta jima ba ta samu sabon rahoton kamuwa da cutar ba, tun a watan Yunin shekarar 2012.

Domin samun nasarar kawar da cutar baki daya daga kasar, gwamnatin Chadi tare da hadin gwiwar kwararru abokan huldarta da masu samar da kudade, ta kaddamar da wani shirin yin allurar riga-kafi ga yara 'yan watanni 3 zuwa 11 a watan Agusta na shekarar 2015.

Sannan a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2016 ne aka bayyana Chadin a matsayin kasar da ba ta dauke da masu cutar ta Polio, sai dai akwai fargaba game da yiwuwar kamuwa da kwayoyin cutar ta polio. Mahukuntan kasar Chadi da abokan huldarta sun sha alwashin daukar dukkan matakai na hana sake barkewar cutar a nan gaba a kasar.

Sakamakon gabatar da wannan sabon shirin riga kafin cutar ta polio, kasar tana burin samun shaidar kasa da kasa ta shekarar 2018.

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF), da hukumar lafiya ta duniya WHO, suna tallafawa gwamnatin Chadin wajen samar da alluran riga-kafin yaki da cutar ta polio, musamman wajen bada horo ga jami'an kiwon lafiya domin su samu nasarar aiwatar da riga-kafin musamman a yankunan marasa galihu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China