in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin-gwiwar Sin da Chadi ta samu manyan nasarori
2017-01-16 11:04:18 cri
Ministan harkokin wajen kasar Chadi wanda ya halarci taron koli na Faransa da Afirka karo na 27 a birnin Bamako na kasar Mali, yayin da ya zanta da 'yan jaridun kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xin Hua kwanakin baya, Moussa Faki Mahamat cewa ya yi, Sin babbar aminiya ce ta Chadi, kuma hadin-gwiwar kasashen biyu ta samu manyan nasarori. Haka kuma malam Faki ya godewa gwamnatin kasar Sin saboda muhimmiyar rawar da ta taka a fannin taimakawa Chadin don samun ci gaba.

Malam Faki ya ce, kasashen Sin da Chadi suna gudanar da ayyukan hadin-gwiwa a fannoni da dama, ciki har da sana'ar man fetur, da ababen more rayuwar al'umma, da titunan mota da gadoji, makamashi da dai sauransu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China