A cewar mista Bachir, wannan cibiya za ta taimaka wajen tabbatar da karin hadin gwiwa da yin amfani da jami'an tsaro yadda ya kamata. Za ta taimakawa wajen kimanta dukkan matsalolin tsaro cikin lokaci a fagen daga, da daukar matakan da suka dace da kuma tattara kayayyakin da ake bukata tsakanin ofisoshin ministocin dake kula da harkokin tsaron jama'a, hukumomin gwamnati da shugabannin rundunonin abin ya shafa.
A cewar madam Mariam Mahamat Nour, ministar tattalin arziki da fasalin kasa, wannan cibiya tana wakiltar tushen tsakiyar wani matakin dake kunshe da dukkan bangarori uku na jami'an tsaron cikin gida wato 'yan sanda, jandarma da gume, a bangaren hedkwatar kasa da kuma sauran 'yankuna 23 da kasar take da su. (Maman Ada)