in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chadi: An kaddamar da kamfen allurar shan inna
2016-11-14 15:50:02 cri
Sakataren gwamnatin Chadi a ma'aikatar kiwon lafiya, Mahamat Annadif Youssouf, ya kaddamar a ranar Lahadi a Pala dake yankin Mayo-Kebbi a yammacin kasar, mai iyaka da Kamaru, da zagaye na hudu na kamfen rigakafin cutar shan inna.

Domin mayar da martani kan nau'o'in kwayoyin cutar da aka gano a jihar Borno ta Najeriya, mai iyaka da kasar Chadi, a cikin watan Augustan shekarar 2016, ma'aikatar kiwon lafiyar jama'a, tare da hadin gwiwar kungiyoyin UNICEF da OMS, sun kaddamar a ranar 16 ga watan Satumba da wani kamfen allurar rigakafi shan inna har sau biyar akai akai.

Kamfen bayan nan, da aka kaddamar a Pala, zai kwashe tsawon kwanaki hudu. Haka kuma yana gudana tare da bada karin sanadarin Vitamin A da kuma aikin kwashe kwayoyin cuta.

A tsawon wadannan kwanaki hudu, ma'aikatan kiwon lafiya zasu bi gida gida da wuraren taron jama'a domin bayar da digo biyu na maganin shan inna ga jarirai zuwa yara masu watanni 59 kusan miliyan 3.3 dake yankuna goma sha biyar na kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China