in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chadi zata sami wani sabon kundin haraji
2016-11-30 10:42:35 cri
Ministan kudi da kasafin kasar Chadi, Mbogo Ngabo Seli, ya gabatar a ranar Talata a N'Djamena, babban birnin kasar, da wani kundin tafiyar da harkokin haraji, da aka yi wa gyaran fuska bayan shekaru goma ana aiki da shi. An ce a wannan karo an samu damar hada dokokin haraji a cikin kundi guda.

Sabon kundin haraji na kunshe da dukkan dokokin kudi daban daban na shekarar 2006 zuwa shekarar 2016, doka kan harajin TVA da kuma kundin tsarin haraji na da.

A cewar mista Mbogo Ngabo, amincewa da wannan sabon kundin haraji na shiga baki daya cikin tsarin gyaran harkokin hada hadar kudin gwamnati da aka fara tun yau da shekaru da dama, kuma yana cikin tsarin hanyar mai da hankali kan damuwar kasar na neman a lokaci guda hanyoyin yawaita tattalin arzikinta, da kyautata yanayin harkoki da kyautata musammun ma kudin shiga bayan man fetur.

Rashin wani kundin da ya shafi harkokin haraji dake shigar da sabbin tsare tsare na baya bayan nan da ake aiki da su a cikin dokokin kudi dadan daban na shekarar 2007 da shekarar 2016, ya janye wani rashin tsaron doka da haraji ga masu amfani, da 'yan kasuwa, kuma zai iya ko shakka babu na barin tsammanin ganin ana wata aiwatarwa bisa zabi, kan rashin adalci ga dokokin haraji daga ma'aikatan dake kula da karbar haraji, in ji mista Mbogo Ngabo Seli. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China