in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Chadi ta amince da wani rancen kudin dalar Amurka miliyan 20 domin ayyukan gina kasa
2016-10-23 13:13:57 cri
'Yan majalisun Chadi sun rattaba hannu a ranar Jumma'a kan wani rancen kudin da ya shafi gina kananan madatsun ruwa a yankunan karkara dake tsakiya da gabashin kasar,a cewar wata majiyar malisar dokoki.

Bisa jimillar dalar Amurka miliyan 20, wannan yarjejeniyar rancen kudin zata taimakawa wajen gina kananan madatsun ruwa a cikin yankuna uku na kasar wato Gurera, Ouaddai da kuma Wadi Fira. Haka kuma aikin zai shafi mutane dubu 180 wadanda kuma kashi 95 cikin 100 suke rayuwa a yankunan karkara.

Shirin ya hada da ayyukan injiniya domin gina gine ginen ruwa da na noma da kiwo, bada tallafi ga makiyaya da manoma, da kungiyoyin manoma, tallafin hukumomi da ayyuka. Wannan ya shafi kara karfin manoma da kudin shigarsu, daidaita muhallin halittu ta yadda za a kula da albarkatun muhalli yadda ya kamata.

Ministar tattalin arziki da fasalin cigaban kasar Chadi, madam Mariam Mariam Nour, ta bayyana imanin cewa wannnan shiri zai ingiza noma da kiwo a yankunan da wannan aiki ya shafa domin jin dadin al'ummomi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China