in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawar zuba jari ga kasashen Afrika karo na 2
2016-09-08 13:59:04 cri

An bude taron dandalin tattaunawar zuba jari ga kasashen Afrika karo na 2 daga yau Alhamis zuwa gobe Jumma'a a birnin Guangzhou na kasar Sin, inda mataimakin firaministan kasar Sin Ma Kai, ya ba da shawarar inganta hadin gwiwa tare da kasashen Afrika da zuba jari a kasashen nasu a fannoni daban daban. Ya kuma nanata cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da sada zumunta tare da kasashen Afrika a fannoni da dama domin taimaka wa juna da biyan bukatunsu.

A shekaru fiye da 10 da suka gabata, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika yana samun bunkasuwa cikin sauri. Sin ta kasance abokiya mafi muhimmanci ta Afirka a fannin cinikayya a cikin shekaru 7 da suka gabata. A halin yanzu dai, kamfanonin Sin fiye da 3100 na raya ayyukansu a kasashen Afrika, wadanda suka shafi fannonin samar da wutar lantarki da makamashi da zirga-zirga da dai sauran muhimman ababen more rayuwa.

Gwamnatin lardin Guangdong, da bankin raya kasa na Sin, da bankin duniya su ne suka shirya wannan dandalin tattaunawa tare. Kafin wannan kuma, lardin Guangdong ya taba kulla yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa da zuba jari guda 9 tare da kasashen Masar da Afrika ta kudu da Habasha da Uganda da Saliyo da Ghana da Congo Kinshasa, wadanda suka shafi sana'o'in zirga-zirgar jiragen sama da samar da wutar lantarki da kera motoci da tufafi da kuma kamun kifi.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China