Kasar Sin na da niyyar samun kilowatt miliyan 58 na karfin makamashin nukiliya dake aiki da kuma sama da kilo watt miliyan 30 da ake aikin samar da su kafin karshen shekarar 2020.
A cewar ministan kare muhalli na kasar, a yanzu, Sin na amfani da na'urorin sarrafa makamashin nukiliya 36, inda kuma ta ke aikin gina wasu sabbi guda 20, adadi mafi yawa da ake aikin samar wa a duniya .
A cewar shirin, ya zuwa shekarar 2020, za a kara inganta kare makamashin kasar ta yadda za a rage yawa hadarin turirin nukiliya tare da kara inganta ayyukansa lokacin da ake bukatar daukin gaggawa.
Ya kara da cewa, zuwa shekarar 2025 kuma, Sin za ta samar da wani tsari na zamani na kare makamashinta da kuma tinkarar hadarin gurbataccen yanayi sakamakon iskar makamashi.
Shirin ya kuma lashin takobin inganta aikin bolar makamashin ta yadda zai dace da ci gaban masana'antar sarrafa makamashin nukiya. (Fa'iza Mustapha)