in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana kudurinta na tabbatar da tsaron makamashin nukiliya
2017-02-15 10:13:41 cri

Kasar Sin ta bayyana cewa, za ta yiwa matakanta na tsaron makamashin nukiliya gyaran fuska, a wani mataki na kara inganta wannan fanni.

Sauran fannonin sun hada da bunkasa shirin ko-ta-kwana tare kuma da inganta yadda ake sarrafa man da aka yi amfani da shi.

Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin kimiyya da masana'antun kera na'urorin tsaro na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Wang Yiren shi ne ya bayyana hakan jiya Talata. Yana mai cewa, kasar Sin za ta gudanar da wasu ayyukan da ke da nasaba da makamashin nukiliya, a yayin da take aiwatar da shiri na 13 na raya kasa daga shekarar 2016 zuwa ta 2020.

Mr. Wang wanda har ila shi ne mataimakin shugaban hukumar kula da makamashin Atom ta kasar Sin, ya kuma ce za a gudanar da bincike game da yadda za a alkinta man da aka riga aka yi amfani da shi.

Da ya ke karin haske game da tsaron tashoshin makamashin nukiliya da za a gina a kasar kuwa, Mr. Wang ya ce gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka dace na ganin an kaucewa aukuwar duk wani hadari.

Jami'in ya ce, gwamnati ta kuduri aniyar kara gina tashoshin makamashin nukiliya ne, sakamakon karuwar bukatar makamashi a sassa daban-daban na yankunan kasar ta Sin.

Yanzu haka gwamnati ta shirya tattaunawa da kwararru kan yadda za a gina tashar makamashin nukiliya a kan teku, domin tallafawa shirin kasar na hako mai da iskar gas ta ruwa da kuma yankunan tsibiran kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China